✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saruniyar Denmark ta kamu da COVID-19 bayan halartar Jana’izzar Sarauniyar Ingila

Sarauniyar kasar Denmark Magrethe II ta harbi da cutar COVID 19 bayan dawowarta daga jana’izar sarauniyar Ingila Elizabeth ta II.

Sarauniyar kasar Denmark Magrethe II ta harbi da cutar COVID 19 bayan dawowarta daga jana’izar sarauniyar Ingila Elizabeth ta II.

Wata sanarwa da fadar Sarauniyar ta fitar ta ce, an yi mata gwajin cutar ne a daren Talata bayan dawowarta daga taron jana’izar takwararta ta Ingila, wadda manya-manyan shugbannin kashen duniya suka halarta.

Sakamakon haka sarauniyar ta soke duk wata ganawa da kuma sauran ayyuka na mulki da ta shirya, in ji sanarwar.

A yanzu Yarima Mai Jiran gado, babban da ga sarauniyar, Frederik da matarsa Mary ne za su wakilce a jagorantar liyafar cin abincin dare da ta shirya da wasu manyan jami’an gwamnatin da kuma ’yan majalisar kasar a ranar Laraba.

Sarauniya Magrethe ta taba kamuwa da kwayar COVID-19, wnada aka gano a watan Fabrairu bayan da aka yi mata gwajin cutar, an kuma yi mata alluran rigakafin cutar har sau uku.

A yanzu dai Sarauniyar Denmark mai shekara 82 a duniya, ta shafe shekaru 50 kan karaga wanda hakan ya sa ta zama wacce ta fi kowanne sarki dadewa a kan mulki a duniya, bayan rasuwar Saruniyar Ingila da ta yi shekara 70.