✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar alade ta jawo wa matashi daurin shekara 1 a kurkuku

Sai dai an ba matashin zabin biyan tarar N10,000

Wata kotun yanki da ke Jos, babban birnin Jihar Filato a ranar Talata ta yanke wa wani matashi hukuncin daurin shekara daya, bayan ta same shi da laifin satar alade.

Kotun dai ta sami Stephen John, mai shekara 24 a duniya da laifin satar aladen da nufin sayar da shi.

Sai dai Alkalin kotun, Mai Shari’a Thomas Ajiyar, ya ba matashin zabin biyan tarar Naira 10,000 bayan ya amsa laifinsa.

Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Insfekta Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotun cewa wani mai suna Aken Galadima na unguwar Rock Haven da ke Jos ne ya kai karar matashin ga ofishin ’yan sanda na “Division A”, ranar 20 ga watan Disamban 2022.

Ya ce Stephen ya saci aladen ne daga wani mai suna Michael Omolara, kafin ya tafi da niyyar sayar da shi.

Laifin, a cewar dan sandan, ya saba da sashe na 57 na kundin Penal Code na Jihar ta Filato. (NAN)