✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar dalibai: UNICEF ya ja kunnen Najeriya

UNICEF ya ce idan ba a hanzarta daukar mataki ba. za a shiga wani bala'i

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadin cewa Yammaci da Tsakiyar Afirka na daf da fadawa cikin wani bala’i idan ba a yi hobbasa don kawo karshen satar yara ’yan makaranta ba.

Shugabar Asusun, Henrietta Fore, ta bayyana haka a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya ranar Laraba yayin da take nuna damuwa a kan sace wasu dalibai a Jihar Kaduna ta arewacin Najeriya.

“Wajibi ne a yi dukkan mai yiwuwa don kawo karshen wannan balahira da ke addabar yara, ganin cewa yankin na daf da fadawa cikin wani mummunan bala’I”, inji ta.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito mai magana da yawun Sakatare Janar na Majalisar ta Dinkin Duniya, Stephane Dujarric, yana shaida wa manema labarai hakan.

Ranar Litinin ne dai ’yan bindiga suka sace wasu dalibai fiye da 100 daga wata makarantar sakandare mai suna Bethel Baptist School a jihar ta Kaduna.

‘Dole a dauki mataki’

Dujarric ya ce Fore ta ambato rahoto na baya-bayan nan na Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya nuna cewa kashi daya bisa uku na yaran da suka fuskanci mummunan tashin hankali a duniya a yankin Yammaci da Tsakiyar Afirka suke.

“Ta ce yin Allah-wadai da wannan aika-aika bai wadatar ba, sannan ta jaddada cewa hakki ne a kan ’yan bindiga-dadi da sauran kungiyoyin da ba na hukuma ba masu dauke da makamai su daina kai hari a kan yara nan take”, inji shi.

Bugu da kari, a wata sanarwa da ta fitar ranar Larabar, Ms Fore ta ce ga alama wadannan al’amura karuwa suke yi ba kakkautawa, tana mai nuna fargaba game da aminci da walwalar yara a yankin.

“Mun damu matuka cewa, kamar a shekarun baya, mai yiwuwa miyagun ayyukan kungiyoyin da ba na hukuma ba masu dauke da makamai a kasashen Burkina Faso da Kamaru da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo da Nijar da Najeriya su karu a makwanni masu zuwa – musamman gabanin faduwar damuna, lokacin da ambaliyar ruwa za ta takaita zirga-zirgarsu”, inji ta.

Fore ta kuma jero misalan hare-haren da aka kai a yankin da satar mutane da sauran tashe-tashen hankali wadanda suka shafi yara a ’yan watannin nan, sannan ta jaddada cewa dole ne a dauki matakin tabbatar da cewa yara na rayuwa cikin aminci.

Abin yi

“Wannan [matakin] ya fara daga kan kungiyoyin masu dauke da makamai wadanda ke tauye hakkokin yara.

“Dole ne su daina kai hari a kan farar hula, su martaba su kuma kare farar hula yayin duk wani fito-na-fito.

“Sannan kuma kada su yi kafar ungulu ga yunkurin UNICEF da sauran kugiyoyin bayar da agaji na kai taimakon jinkai ga yara marasa galihu”, inji ta.

Ta kara da cewa kasashen duniya ma na da rawar da za su taka, ciki har da ta hanyar kara yawan taallafin da suke bai wa kungiyoyin agaji saboda su samu damar fadada ayyukansu.