✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa muke adana kayan abincin —FEMA

Hukumar Agaji ta Birnin Tarayya (FEMA) ta ce gwamnati na sayen kayan abinci ta adana a rumbunanta ne, saboda idan bukata ta taso ba sai…

Hukumar Agaji ta Birnin Tarayya (FEMA) ta ce gwamnati na sayen kayan abinci ta adana a rumbunanta ne, saboda idan bukata ta taso ba sai ta shiga kasuwa ta siyo ba.

Shugaban FEMA, Alhaji Abbas Idris, ya ce wani lokacin idan ’yan kasuwa sun kara farashin kayan abinci, gwamnati kan fito da nata domin ta karyar da farashi don a saukaka wa jama’a.

A hirar da shirin ‘Bakin zare’ na tashar NTA Hausa ya yi da shi, Alhaji Abbas ya ce gwamnati kan sayi kayan abinci ta ajiye don shirin ko-ta-kwana da zai sa jama’a neman tallafin gwamnati ba wai saboda annobar COVID-19 ba.

Ya yi tir da matasan da suka farfasa wuraren ajiyar abincin gwamnati da na ’yan kasuwa da sunan dibar ganimar kayan abincin gwamnati.

Shugaba hukumar ya ci gaba da nuna takaicin barnar da matasan suka yi a matsayin wata asara da za a jima ba a mayar da abun da aka rasa ba.

Ya bayar da misali da barnar da aka yi a jihar Legas, inda asarar ta kazanta da kuma abun da matasa suka yi a rumbunan ajiyar abincin a sauran jihohi.

“Mun zaga da Ministan Birnin Tarayya, Muhammad Bello, wuraren ajiyar gwamnati da na kamfanoni masu zaman Kansu da abun ya shafa.

“Abun takaicin ya yi yawa, mun tarar da wata ma’ajiyar wani kamfani a rukunin masana’antu na Idu da ke nan Abuja, inda mai kamfanin ya ce an sace tare da barnata musu kayan da suka kai na Naira biliyan daya.

“Wannan kamfanin matasa yake dauka aiki a ciki; Yanzu a dole su rage ma’aikata saboda ba za su iya daukar nauyin da suka dauka a baya ba sakamakon wannan barnar.

“Yanzu matasa marasa aikin yi sun karu ko sun ragu?”