✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar iPhone: Kotu ta daure matashi a gidan yari

Wata kotun Majistare ta daure wani matashi mai shekara 22 a gidan yari na tsawon shekara daya bayan ta kama shi da laifin zamba da…

Wata kotun Majistare ta daure wani matashi mai shekara 22 a gidan yari na tsawon shekara daya bayan ta kama shi da laifin zamba da kuma satar wayar salula kirar iPhone.

Alkalin kotun, Mai Shari’a A.A. Ayeni, yayin da yake hukunci ya kama wanda ake zargin da aikata laifukan sata da zamba cikin aminci.

Mai Shari’a Ayeni, ya kuma ba shi damar zabar biyan kudi N10,000 kan kowane laifin da ake cajin sa da shi.

Tunda farko, dan sanda mai gabatar da kara, Sunday Osanyintuyi, ya fada wa kotu cewa matashin ya sace wayar salula guda daya, kirar iPhone 8plus, da ta kai kimar kudi N166,000 mallakar Adediwura Ogunleye.

“Har-ila yau, ana zarginsa da zambar kudi N50,000 na wani mutum daban mai suna Shittu Samuel, inda ya zambace shi da sunan zai  biya masa kudin hayar gidan da yake zaune, amma ya kashe N50,000 din mutumin a sabgar gabansa,” inji shi.

Ya ce matashin ya aikata laifin ne a ranar 18, ga watan Nuwambar 2020 da misalin karfe 11 na safe a unguwar Mayfair dake Ile-Ife.

Osanyintuyi, ya kara da cewa aikata hakan ya saba da sashe na 383,390 (9) da 419 na kundin dokokin hukunta masu laifin na Jihar Osun, 2002.