✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Satar kayan tallafi: An samu gawar mutane hudu a cikin dam 

An tsinci gawar mutum hudu da suka fada Dam din Laminga, domin gudun kada jami’an tsaro su cafke su saboda wawushe kaya da suka yi…

An tsinci gawar mutum hudu da suka fada Dam din Laminga, domin gudun kada jami’an tsaro su cafke su saboda wawushe kaya da suka yi a gidan tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara.

A makon jiya ne zauna-gari-banza suka shiga gidan Dogara da ke daura da Dam din Laminga a garin Jos, suka sace abubuwan amfanin yau da kullum a gidan.

Kakakin Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, Omini Bridget, ta tabbatar wa da wakilinmu cewa an kai gawarwakin mutanen da aka samu a Dam din na Laminga.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa gawarwakin guda takwas ne, an dauki wasu zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, wanda suka rasun, sun tsere ne tare da fadawa dam din, domin guje wa fadawa hannun jami’an ’yan sanda.