✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar mutane: Masu zanga-zanga sun tare hanyar Abuja

Masu zanga-zangar da ke zargin gazawar gwamanti sun kona ofishin ’yan sanda.

Mutanen garin Gauraka a Jihar Neja sun tare babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja domin nuna fushinsu kan yawaitar garkuwa da mutane a yankin.

Tun da sanyin safiyar Litinin masu zanga-zangar suka tare hanyar saboda abin da suka kira gazawar gwamnati ta kare su daga masu garkuwa da mutane.

 

Masu boren sun kona Babban Ofishin ’Yan Sandan garin, har da motoci da sauran ababen hawa da ake harabar da ma kusa da shi.

Kimanin wata biyu da suka gabata an yi sace mutum shida a garin, sai da aka biya kudin fansa Naira miliyan biyu kafin aka sako su.

Kwana biyar da suka wuce kuma an sake yi garkuwa da wasu mutum hudu, sannan a ranar Lahadi ’yan bindiga sun kai hari tare da garkuwa da mutum 16 a garin na Gauraka.

Zanga-zangar ta haifar da cunkoson ababen hawa daga Gauraka har zuwa barikin sojoji na Zuma da kuma unguwar Madalla da ke kan babban hanyar.

A wani labarin kuma, an kona wata mota dauke da wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne ko masu fashi da motoci da ake kira ’yan ‘One Chance,’ a Madalla.