✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar mutane: Matan Kaduna sun tare hanyar Abuja

Mata masu zanga-zanga sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja saboda satar mutane a Jihar Kaduna.

Mata sun gudanar da zanga-zanga tare da tare babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja saboda garkuwa da mutane a Jihar Kaduna.

Fusatattun matan sun tare babbar hanyar ce a daidai unguwar Gonin Gora, bayan ’yan bindiga sun sace mutum hudu da dare kafin wayewar garin Asabar a Unguwar Auta a yankin na Karamar Hukumar Chikun.

Zanga-zangar matan domin nuna bacin ransu kan yadda satar mutane ta zama ruwan dare a Jihar ta haifar da cunkoson ababen hawa na tsawon sa’o’i a kan hanyar a ranar Asabar.

Matafiya masu zuwa ko dawowa Kaduna daga Abuja sun yi ta sauya hanya suna bi ta kauyen Juji domin kauce wa cunkokon ababen hawa da zanga-zangar ta haddasa.

Aminiya ta gano cewa rundunar tsaron hadin gwiwa a jihar ta yi nasarar kwato biyu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su bayan musayar wuta da ’yan bindigar.

Wani shugaban rundunar ya ce karo na shida ke nen da ’yan bindiga suke garkuwa da mutane a yankin na Gonin Gora.

“Matan sun fito ne domin su nuna fushinsu game da garkuwa da mutanen, amma an riga an bude hanyar tun da safe,” inji shi.

Shi ma wani mazaunin yankin, ya ce zanga-zangar ta gudana ne cikin lumana, kuma sako ne ga gwamnati.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, amma bai amsa kiran wayarsa ba.