✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar yara a Kano: Kotu ta umarci a kamo wasu mutane

Rashin bayyanar wasu daga cikin wadanda ake zargi da satar wani yaro a Kano, wata babbar kotu a jihar ta ba da uamarnin cafko wasu.

Wata babbar kotu a Kano ta bayar da umarnin kamo wasu mutum uku da ake zargi da kin bayyana a gabanta don amsa tuhuma akan satar yara.

Wadanda ake tuhumar sun hada da wata mata da ake zargi da hada baki da wasu mutum bakwai wajen aikata laifin.

Sa dai zaman kotun na Mai Shari’a Dije Aboki ya samu tsaiko saboda daya daga cikin mutum bakwai da ake zargi da hada baki ba ta jin Turanci ko yaren Pidgin, sai dai yaren Igbo kawai.

Lauya mai gabatar da kara, Barista Tijjani Ibrahim ya nemi kotun ta yanke hukunci a kan sauran wadanda ake zargin wadanda da ma ta ba da belinsu.

Mai Shari’a Aboki ya bukaci gwamnain jihar Kano da ta samar da mai tafinta a zaman kotun na gaba wanda ya dage zuwa 25 ga Nuwamba.

Aminiya ta ruwaito cewa ana zargin mutanen ne da hada baki da wasu suka sace wani yaro mai shekara 2 wanda ya mutu a hannunsu, kuma hakan laifi ne a sashi na 97 da 273 na kundin laifuka.

Wadanda ake zargin an kamo su ne a unguwar Kawon Lambu ‘B’ a Karamar Hukumar Nassarawa da ke Jihar Kano a 2017.