✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar yara: Shin laifin iyaye ne?

A makonnin nan ne aka rika bankado matsalar satar kananan yara da aka rika kaiwa Kudu musamman Jihar Anambra daga nan Arewa.Wannan lamari ya ja…

A makonnin nan ne aka rika bankado matsalar satar kananan yara da aka rika kaiwa Kudu musamman Jihar Anambra daga nan Arewa.Wannan lamari ya ja hankalin jama’a sosai, bayan da Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta samu damar gano wadansu yaran da aka sace a Jihar Anambra. Sai dai a wani taro da aka gabatar Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa wannan matsala ta satar yara daga nan Arewa zuwa Kudu laifin iyayen yara ne. Maganar tasa ta jawo cece-ku-ce a tsakanin jama’a, hakan ya sa wakilanmu suka jiyo ra’ayoyin al’umma a kan wannan magana: 

 

Ba laifin iyaye kadai ba ne –Nura Abubakar

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Na farko idan dan masu hannu da shuni aka sata, sai a ce laifin jam’ian tsaro ne, sakacinsu ne. Amma idan dan talaka aka sata, sai a dora laifin a kan iyaye a ce ba sa kula da ’ya’yansu. Ban ki ba yana iya yiwuwa akwai sakacin iyaye, don dama hakkinka ne ka kula da yaranka, ka san ina suke zuwa. A daya bangaren kuma su ma jam’ian tsaro suna da nasu hakki domin suna kula da al’umma. Kamata ya yi shi Sarki idan ya taba bangaren iyaye sai ya tabo sakacin hukuma na gazawar jam’ian tsaron wajen kare rayuka da kula da hakkin da ke wuyansu na kula da al’umma. Ka ga da ya yi haka da shi ne ya fi daidai.

 

Laifin iyaye ne – Abba Last Talk

Daga Muhammad Aminu Ahmad

A Gaskiya iyaye suna da laifi na kasa kulawa da yaransu, don haka maganar da Sarkin Kano ya yi, ina goyon baya, don za ka ga iyaye ba sa kula da tarbiyar ’ya’yansu, sun bar su suna yawo ko’ina, kuma sun san cewar hakki ne a kansu kula da tarbiyyar ’ya’yan nasu. Kuma dole ne iyaye su rika sa ido a kan inda ’ya’yansu suke zuwa, kai idan da hali a rika hada su da manya don gudun faruwar wani abin ki.

 

Ba laifin iyaye ba ne – Muhammad Kabir Ibrahim (KB Suya)

Daga Ibrahim Babangida Surajo

Wannan ba gaskiya ba ne, ta yaya yaran da aka sace a cikin unguwanninsu ko a gaban makarantunsu kuma a ce laifin iyayensu ne.  Wannan wani zan ce ne da muka saba jin irinsa daga bakin Sarkin Kano.

 

Laifin har da na al’umma–Shafi’u Iliyasu Ahmad

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Ni ina ganin bayan laifin iyaye akwai kuma na al’umma, domin ba komai ne za a ce gwamnati za ta kula da shi ba. Idan mun duba ’yan sanda nawa muke da su da za su tsare dukkan al’ummar da ke kasar nan?  Su kuma iyaye dole ne su tsaya su dage wajen kula da ’ya’yansu. Za ki ga an saki wadansu yaran a unguwa ko sutura babu a jikinsu da sunan sun fito wasa. Iyaye ba za su tashi neman ’ya’yan nan ba sai lokacin da suka gama abinci ne a za a farga cewa yaran ba su nan. Daga nan a fara nemansu. Wannan ba daidai ba ne. Ya kamata mu farka mu san cewa yanzu lokaci ya canja.

 

Ba laifin iyaye ba ne –Nura Mai Bulo

Daga Ibrahim Babangida Surajo

Ni ban amince da cewa laifin iyayen yara ba ne kamar yadda Sarkin Kano ya fada. Saboda babu yadda za a yi a ce duk inda yaronka zai tafi a cikin unguwa sai ka raka shi. Akwai yaran da ma aka sace a cikin gidajensu. Ba laifi ba ne idan aka ce iyaye su kara kula da yaransu amma ba a dora musu laifi ba.

 

Laifin na iyaye ne – Sani Yusuf

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Babu shakka ni ma na fadi cewa laifin iyaye ne domin idan mutum ya killace dansa babu wanda zai shigo gida ya daukar masa da. Amma za ka ga yaro ya fito yana yawo ba tare da iyaye sun san wurin da suke ba. Ko batun tura yara makaranta da kansu akwai sake a cikinsa. Ya kamata iyaye su dauki nauyin kai yaransu makaranta tare da dauko su idan an tashi.  Iyaye su tuna fa ’ya’ya kiwo ne da Allah Ya ba mutum dole ne mutum ya lura da kiwon da aka ba shi domin Allah zai tambaye shi a kan abin da ya ba shi kiwon