✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar yaro: Kotu ta yi wa fasto daurin rai-da-rai

Kotu ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai a kan wani fasto da wani yaro mai shekara daya Gold Kolawole, ya yi batar dabo a cocinsa. Babbar…

Kotu ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai a kan wani fasto da wani yaro mai shekara daya Gold Kolawole, ya yi batar dabo a cocinsa.

Babbar Kotun Jihar Ondo ta yanke wa Fasto Samuel Babatunde wanda shi ne ya assasa cocin Sotitobire Praising Chapel, hukuncin ne a ranar Talata.

Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Olusegun Odusola ya ce “hujjojin da masu kara suka gabatar” sun tabbatar wadanda ake zargin sun aikata laifuka biyu na hada baki da kuma garkuwa da mutane.

An sace yaron ne a lokacin da ake gudanar da ibada a cocin da ke Akure a watan Nuwamban 2019 kuma har yanzu babu labarainsa.

Sakamakon haka ne aka tsare Fasto Babatunde da wasu mabiyansa bakwai aka kuma gurfanar da su kan zarge-zarge shida.

Bayan sauraron karar a Kotun Majistare da ke Garin Akure ne aka mayar da shari’ar zuwa Babban Kotun Jihar.

Sauran wadanda kotun ta yanke wa hukuncin daurin su ne Omodara Olayinka, Margaret Oyebola, Grace Ogunjobi, Egunjobi Motunrayo da kuma Esther Kayode.

Idan za a iya tunawa a watan Disamban 2019 wasu fusatattun matasa sun kona cocitin Sotitobir Miracle Centre bayan wani rahoto da ke cewa an kashe yaron ne a binne shi a mimbarin cocin.

Daga bisani ‘yan sanda suka karyata rade-radin da ke cewa an hako gawar yaron a cocin.