✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Sau 3 ina yunkurin kashe mahaifina saboda na ci gado’

Har na mallaki bindigar, sai na je wani wuri ina gwada koyon harbi a iska, sai kwatsam ’yan sanda suka kama ni.

’Yan sanda sun cafke wani matashi mai shekaru 25 a Unguwar Gadon Kaya da ke Karamar Hukumar Gwale ta Jihar Kano.

Matashin wanda aka kama da wata karamar bindiga, ya ce sau uku yana yunkurin kashe mahaifinsa domin ya gaji dukiya ya yi bushasha kamar yadda ya ga abokansa suna yi.

Matashin ya ce tun a shekarar 2018 ya daura damarar ganin bayan mahaifinsa, yayin da daga cikin  abokansa ya ci gajiyar kudi masu yawan gaske bayan rasuwar mahaifinsa har ya sayi babur.

A jawabinsa yayin da ’yan sanda ke yi wa manema labarai holensa a birnin Dabo, matashin ya ce, “Mahaifina mutumin kirki ne kuma yana kaunata.

“Yana ba ni kulawa da sauke duk wani nauyi da ya rataya a kan kowane uba da ke son ’ya’yansa, amma dai na yi yunkurin kashe shi don na gaje kudin da ya tara.

“Tun daga lokacin da mahaifin wani abokinmu ya rasu, kuma bayan an raba musu gado ya samu kudi masu yawan gaske, to daga nan ne na fara tunanin kashe nawa mahaifin.

“A karon farko da na yi yunkurin kashe shi shi ne a shekarar 2018 lokacin ina Makarantar Sakandire.

“A wannan lokaci na yi amfani da shinkafar bera amma ya tsira. Na sake maimaita wannan dabara shi ma ban samu biyan bukata ba.

“A wannan karo, motarsa na dauka ba tare da izininsa ba kuma tsautsayi ya sa na yi hatsari da ita.

“Yanzu watanni uku ke nan ban iya komawa gidanmu ba. Sai na yanke shawarar mallakar bindiga na harbe shi da ita kawai na cimma burina.

“Sai wani abokina ya ce akwai wata bindiga ta sayarwa idan ina so na mallaka sai mu yi amfani da ita.

“Har na mallaki bindigar, sai na je wani wuri ina gwada koyon harbi a iska, sai kwatsam ’yan sanda suka kama ni.”