✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sau 66 muna dakile yunkurin yi wa taron Majalisar Zartarwa kutse  —Pantami

Sau 66 ana yunkurin yi wa taron Gwamnatin Najeriya kutse daga ketare.

Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Pantami ya bayyana cewa sun dakile kutse 66 da aka yi yunkurin yi wa taron Majalisar Zartarwa ta intanet.

Pantami wanda ya ce tushen kutsen daga ketare ne kuma an sanar da duka batutuwansu ga hukumomin da suka dace don daukar mataki.

“Aikinmu a sha’anin tsaron intanet shi ne tabbatar mun takaita aikata manyan laifuka ta amfani da fasahar zamani,” in ji shi.

Ministan ya bayyana haka ne a wajen taron auna ayyukan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari karo na 19 da aka gudanar a Abuja.

Ya ce tun bayan samuwar dokar yin taro ta intanet ga hukumomin Gwamnatin Tarayya a 2020, an gudanar da taro akalla 108 ta bidiyo ciki har da na Majalisar Zartarwa da sauransu.

Ya ce amfani da wannan tsari ya taimaka wa kasar wajen samun rarar sama da Naira biliyan 47.

Haka nan, ya ce an samar da aiki akalla sama da miliyan biyu a fannin fasahar zamani a tsakanin shekaru ukun da suka gabata.