✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta wajabta wa alhazai yin allurar rigakafin COVID-19

Ma'aikatar Aikin Hajji da Umrah ta ce daukar matakin ya zama tilas

Mahukunta a kasar Saudiyya sun wajabta wa maniyyata aikin Hajji da Umrah yin allurar rigakafin COVID-19.

Ministan Aikin Hajji da Umrah na Saudiyya, Muhammad Saleh Benten ya bayyana hakan ne bayan an yi masa allurar rigakafin cutar.

“Duk wanda ke son yin aikin Umrah ko Hajji dole ne ya yi allurar rigakafin,” inji Ministan.

Ya ce daukar matakin ya zama tilas domin kare yaduwar annobar a tsakanin mahajjata.

Ya kara da cewa za a ci gaba da daukar matakan kariyar cutar da suka hadar da wanke hannaye da sanya takunkumi da kuma ba da tazara.

Wannan mataki na kasar Saudiya na zuwa ne a lokacin da maniyyata da ke sa ran yin Umrah ke yin harama.