✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya na yi wa mutum 440,000 rigakafin coronavirus kyauta

Ma'aiakatar Lafiya ta riga ta tantance mutanen da za a yi wa rigakafin kyauta

Ma’aikatar Lafiya ta kasar Saudiyya ta tantance mutanen da zata fara yi wa rigakafin cutar coronavirus a matakin farko.

Maaikar ta ce ta tantance kimanin mutum dubu 440 da za ta ba fara yi wa rigakafin cutar a fadin kasar.

A kwanakin baya Ma’aikatar Lafiyar Saudiyya ta sanar da cewa za ta samar da wadaccen rigakafin cutar wanda za a yi wa ’yan kasar kyauta.

Mataimakin Sakataren Ma’aikatar, Dokta Abdullah Al-Asiri ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a kowace rana kan annobar coronavirus a kasar.

Al-Asiri ya ce suna sa ran akalla kashi 70 cikin 100 na jama’ar Saudiyya za su amfana da rigakafin kyauta daga yanzu zuwa karshen shekarar 2021.

Ya bayyana cewa kasar na cikin kasashe ashirin na G20, masu karfin tattalin arziki a duniya da suka fara daukar matakan kariya da samar da rigakafin kyauta ga mutanen da suka kamu da cutar.