✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta amince ’yan kasashen waje su je aikin Hajji a bana

Za a sanar da hanyoyin kare kai da za a bi domin kiyaye yaduwar cutar Coronavirus.

Mahukunta Saudiyya sun amince maniyyata daga fadin su je aikin Hajji a wannan shekara tare da tabbatar da an kiyaye tsauraran matakan da aka gindaya na dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Hakan na zuwa ne bayan hukuncin da Hukumar Hajji da Umara ta kasar Saudiyya ta yanke a ranar 9 ga watan Mayu wanda ya ce ya kamata a bar maniyyata su yi aikin a bana bisa la’akari ga sharudan hukumomin lafiyar kasar.

Sashen hausa na BBC ya ruwaito cewa, a farkon watan nan ne Ma’iakatar Lafiya ta Saudiyya ta ce za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa an kiyaye lafiyar duk wanda ya kai ziyarar ibada kasar.

Sanarwar da Ma’aikatar Lafiyar kasar ta fitar ta ce za ta sanar da hanyoyin kare kai da za a bi domin kiyaye yaduwar cutar Coronavirus.

Ana iya tuna cewa, a bayan can kimanin musulmi miliyan 2.5 ne ke zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji duk shekara daga fadin duniya, amma saboda annobar Coronavirus a ka rage adadin zuwa 1000 a bara.