✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta bai wa mata izinin aikin Hajji babu muharrami

Za a rufe rajistar maniyyatan bana a ranar 23 ga watan Yuni.

Hukumomi a kasar Saudiyya sun bai wa mata damar neman izinin yin aikin Hajjin ban aba tare da muharrami ba.

Ma’aikatar Kula da Aikin Hajji ce ta sanar da hakan da cewa mata na iya zuwa da kansu su yi rajistar aikin Hajjin bana ba tare da wani namiji muharraminsu ba.

Sanarwar ta kayyade shekarun matan da za su yi aikin Hajji daga shekara 18 zuwa 65 sannan kuma su kasance sun yi allurar rigakafin cutar Coronavirus.

Aminiya ta ruwaito cewa, Saudiyya ta ce iyaka mazauna kasar ce kadai za su yi aikin Hajjin na bana, a wani yunkuri na ci gaba da yaki da dakile yaduwar annobar Coronavirus.

Sanarwar da Masarautar Kasar ta fitar a ranar Asabar ta ce, mutum dubu sittin ne kacal da suka hada da ’yan asalin kasar da kuma mazaunanta ne za su iya yin rajistar aikin Hajjin na bana.

A ranar Lahadi na aka soma rajistar maniyyatan aikin Hajji wanda za a ci gaba har zuwa ranar 23 ga watan Yunin bana.