✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta bukaci a kawo karshen zubar da jini a Gaza

Saudiyya ta bukaci bangarorin su tsagaita wuta saboda rayuka da ake rasawa.

Ma’aikatar Harkokin Kasashen Wajen Saudiyya, ta bukaci a kawo karshen rikicin yankin Gaza da Gabashin birnin Kudus.

Saudiyya ta nuna goyon bayanta ga Falasdinawa, tare neman kawo karshen zubar da jinin da Isra’ila ke yi.

Ministan Harkokin Wajen Saudiyan, Yarima Faisal bin Farhan, ya ce kasarsa na goyon bayan Falasdinawa kan irin ta’addancin da ake musu.

A cewarsa, kasarsa na goyon bayan samar da halastacciyar kasar Isra’ila a kowane lokaci tare da Gabashin birnin Qudus a matsayin babban birninta, matsayar da kasar ke kai tun 1967.

Yarima Faisal, ya bayyana hare-haren sojin Isra’ilan kan yankin na Gaza a matsayin abin kunya wanda ke rura wutar ayyukan ta’addanci.

Ya bukaci kawo karshen hare-haren daga bangaren Isra’ila da kuma sojin Hamas da ke mayar da martani.