✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta cike rijiyoyi 2,450 bayan rasuwar Rayan

Saudiyya ta cike tare da killace wasu tsoffin rijiyoyi guda 2,450 da aka yi watsi da su.

Kasar Saudiyya ta cike tsoffin rijiyoyi guda 2,450 da aka yi watsi da su, bayan fadawar wani karamin yaro a wata tsohuwar rijiya a kasar Moroko ya yi ajalinsa.

Yaron mai suna Rayan ya rasu ne bayan shafe kwana biyar a cikin tsohuwar rijiyar da ya fada a yayin da aka kwana biyar, ba dare, ba rana, ana aikin ceto shi, amma bayan an fito da shi, rai ya yi halinsa.

Bayan aukuwar lamarin a kauyen Ighrane da ke kasar Moroko, Ma’aikatar Muhalli, Albarkatun Ruwa da Noma ta Saudiyya ta sanar, cewa, “Domin tabbatar da tsaron lafiyar al’umma… ma’aikatar ta cike tare da killace tsoffin rijiyoyi 2,450. Za kuma ta ci gaba da cike rijiyoyi marasa murfi.”

Ma’aikatar ta kuma bukaci al’umma da su kawo mata rahoton duk wata rijiya mara rufi ko wadda take da hadari, tana mai cewa, “Bayanan da za ku bayar za su taimaka wajen kare rayukan jama’a.”

Rayan ya fada tsohuwar rijiya ne a ranar Talata, wanda a sakamakon haka aka kaddamar da wani gagarumin aikin kwashe kasa domin ceto shi.

A ranar Asabar aka kammala aikin ceton, a yayin da masarautar kasar ta sanar da rasuwarsa a ranar Lahadi.

A ranar Litinin dubban mutane suka halarci jana’izarsa, a yayin da Sarkin Moroko,  Mohammed VI, kuma ya kira iyayen somin yi musu ta’aziyya.