✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta dage haramcin da ta sa wa jirage daga Najeriya

Hakan dai na nufin ’yan Najeriya za su fara tafiya Umara ke nan.

Kasar Saudiyya ta sanar da dage haramcin da ta sanya wa jirage daga Najeriya zuwa cikinta saboda annobar COVID-19 samfurin Omicron.

Aminiya ta rawaito cewa Saudiyya ta sanya haramcin ne ranar takwas ga watan Disamban 2021, lamarin da ya dakatar da dukkan masu tafiya don aikin Umara daga Najeriya.

Dage haramcin da wasu tsauraran matakan kariyar COVID-19 da dama dai da aka sanar ranar Asabar, wata ’yar manuniya ce kan yiwuwar kyale baki su yi Aikin Hajji a bana.

A cewar wata sanarwar da Aminiya ta gani a shafin Twitter na jaridar Saudi Gazette, Saudiyya ta kuma dage haramcin ga wasu karin kasashe 17.

Kasashen sun hada da Afirka ta Kudu da Namibia da Botswana da Zimbabwe da Lesotho da Eswatini da Mozambique da Malawi da Mauritius da Zambia da Madagascar da Mauritius da Zambia da Angola da Seychelles da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da dai sauransu.

A ranar takwas ga Disamban baran ne dai Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA) ya sanar da dakatar da zirga-zirgar jirage daga Najeriya cikin wata wasika da ta aike wa dukkan kamfanonin jiragen da ke sufuri tsakanin kasashen biyu.

Hakan ne dai ya sa kamfanin jiragen sama na Azman, wanda shi kadai ne yake jigilar ’yan Najeriya zuwa Saudiyyar ya dakatar da duk ayyukan Umara.

Galibi dai musulmi daga Najeriya kan yi tururuwar zuwa Saudiyya musamman da watan azumin Ramadan don gudanar da ibadar Umara a cikinsa.

Matakin na Saudiyya kuma na zuwa ne lokacin da ya rage kasa da mako hudu kafin fara azumin.