✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta gargadi masu daukar hoto a wuraren ibada

Wasu malaman na ganin hakan a matsayin wani nau’i na riya.

Hukumar Kula da Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta yi kira ga masu ziyarar ibada zuwa wurare masu alfarma da su martaba darajar wuraren.

Hukumar ta yi kira ga masu ziyarar da su rika kiyaye dokoki wajen daukar hotunan.

Hukumar ta ce bai kamata masu ziyarar ibadar su bige da daukar hotuna, a maimakon mayar da hankali kan ibadar da ta kai su kasa mai tsarkin.

Haka kuma hukumar ta gargadi masu daukar hotunan da su guji hadawa da wasu mutanen a cikin hoton nasu, ba tare da izini ba.

Sannan ta bayyana cewar masu ziyarar ibadar su daina tsayawa don daukar hoto a wuraren da jama’a da dama suka taru, domin a cewarta hakan na janyo cunkuson jama’a a wuraren.

BBC ya ruwaito cewa, a baya-bayan nan dai mutane sun bullo da salon daukar hotuna a lokacin ziyarar ibada zuwa kasa mai tsarkin tare da wallafawa a shafukansu na sada zumunta.

Lamarin da wasu malamai ke ganin cewa zai iya zama ‘Riya’, abin da kuma a cewar malaman zai iya bata wa mutanen ibadarsu.