✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta janye ka’idar yawan shekaun zuwa Umrah

A sabon tsarin, kowane dan kasar waje na da damar zuwa Saudiyya domin yin Umrah, muddin ya haura shekara 18 a duniya. 

Hukumomin kasar Saudiyya na shirin janye batun yawan shekaru da suka kayyade wa masu zuwa kasar domin yin ibadar Umrah daga kasashen ketare.

A baya Ma’aikatar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bullo da wani tsari da ya hana duk wani dan kasar waje da ya haura shekara 50 a duniya samun izinin gudanar da ibadar Umrah.

Amma a karkashin sabon tsarin, kowane dan kasar waje na da damar zuwa Saudiyya domin yin Umrah, muddin ya haura shekara 18 da haihuwa.

Hakan na kunshe ne a sanarwar da shafin bayar da izinin shiga kasar Saudiyya ta intanet ya fitar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumoin Saudiyya suka ayyana dokar hana shigar baki daga wasu kasashe, bayan bullar kwayar cutar Omicro, wanda nau’i ne na cutar COVID-19.

Miliyoin Musulmai daga sassan duniya ne ke ziyartar Saudiyya a duk shekara domin gudanar da ibadar Umrah da ziyara.

Sai dai bullar cutar COVID-19 ta sa an tataika yawan masu zuwa domin gudanar da ibadar, kafin daga baya a sassauta  dokar bayan an samu raguwar alkluman masu kawamu da ita.

Ana kuma fata da wannan sabuwar dokar za a samu karin masu zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da ibadar ta Umrah.