✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta kai wa mayakan Houthi hari a Yemen

An yi nasarar lalata makamai da dama da ma maboyar mayakan na Houthi.

Mayakan kawance da Saudiyya ke jagoranta a kasar Yemen sun sanar da kai wani farmaki a sansanin mayakan Houthi da ke Sana’a babban birnin kasar a wannan Lahadin, inda suka kashe mutane uku.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya SPA, a wannan harin an yi nasarar lalata makamai da dama da ma maboyar mayakan na Houthi.

Duk wannan na zuwa ne bayan da a ranar Asabar, hukumomi a Saudiyya suka sanar da wasu harin rokoki da ake zargin mayakan Houthi da harbawa a masarautar Saudiyya wanda ya yi sanadin rayukar mutane uku da kuma jikkata wasu da dama.

Bayanai sun ce dai wannan harin shi ke zama irinsa na farko ga masarautar a sama da shekarun uku.

Saudiyya dai ta jima tana zargin kasar Iran da daukar nauyin ayyukan mayakan na Houthi da ma samar musu da manyan makamai.

Tun a shekarar 2014 ne Yemen ta fada cikin yaki tsakanin gwamnati da mayakan na Houthi da ke rike da ikon yankunan arewacin kasar.

Mayakan Houthi sun kashe dakarun Sudan 14 a Yemen

A makon da ya gabata ne wata majiyar sojan Yemen ta ce sojojin Sudan akalla 14 sun rasa rayukansu, a wani hari da mayakan Houthi suka kai a kusa da kan iyakarsu da Saudiyya daga bangaren arewa maso yamma.

Majiyar sojin ta Yemen ta ce an kashe sojojin na Sudan ne lokacin da mayakan suka kai farmaki kan wasu yankunan Haradh da ke lardin Hajja.

Sudan dai na cikin rundunar kawancen sojojin da Saudiyya ke jagoranta da ke goyon bayan gwamnatin Yemen da kasashen duniya suka amince da ita tun shekara ta 2015, inda take gwabza yaki da mayakan Houthi masu samun goyon bayan Iran.

Tun da jimawa ne dai kasar Sudan ta aike da dubban sojoji zuwa Yemen, ciki har da mayakan Janjaweed da suka yi kaurin suna kan zargin da ake musu na aikata munanan laifuka a yakin basasar da ya barke a yankinta na Darfur a shekara ta 2003.

Sai dai a karshen shekarar 2019, gwamnatin rikon kwaryar Sudan ta ce za ta rage yawan dakarunta a Yemen daga 15,000 zuwa 5,000.

Rikicin Yemen da ya faro tun a shekarar 2014 bayan ’yan tawayen Houthi sun kwace babban birnin kasar Sanaa, ya haifar da abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira tagayyarar jin kai mafi muni a duniya.

Miliyoyin mutane sun rasa matsugunansu kuma fiye da kashi 80 na al’ummar kasar ta Yemen kusan miliyan 30 na bukatar agajin jin kai, yayin da mutane akalla dubu 377 suka mutu.