✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta kara wa Najeriya wa’adin jigilar Aikin Hajji

Hukumar NAHCON ta ce wa'adin zai ba ta damar kwashe ragowar maniyyatan da ba su samu zuwa Saudiyya ba

Gwamnatin Kasar Saudiyya ta kara wa Najeriya wa’adin kammala jigilar maniyyata domin gudanar da aikin Hajji a bana.

Wata sanarwa da Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta fitar ranar Laraba, ta bayyana cewa kara wa’adin da Saudiyan ta yi zai ba da damar kwashe sauran maniyatan Najeriya da a baya ba ta samu kaiwa Kasa Mai Tsarki ba.

Kazalika ta ce hakan ya biyo bayan wata doguwar tattaunawa da ta wakana tsakanin Hukumomin Najeriya da na kasar Saudiya, wanda Shugaban NAHCON, Zikrullah Hassan ya jagoranta.

Hakan dai ya haifar da zanga-zangar maniyata musamman a Jihar Kano, wadanda suka biya kudinsu tun a shekara ta 2019.

Hukumar ta ce wannan karin wa’adin zai ba wa kamfanonin jiragen Azaman da Max Air da ke aikin jigilar maniyatan damar kwashe sauran maniyatan da ba su samu tafiya ba a baya.

Ta ce shirye-shiryen sun kammala kamfanin jirgin Flynas domin taimaka mata da jigilar sawu uku na maniyatan Kano da Abuja.

Idan za a iya tunawa dai, tun daga shirye-shiryen fara jigilar maniyatan a Najeriya, matsaloli ke ta kunno kai a hukumar bida zargin rashin shirin da ya kamata tun a matakin jihohi da ma kasa.