✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta kashe matashi kan laifin da ya aikata yana karami

Ana zargin ya aikata laifin ne a lokacin da shekarunsa na haihuwa basu wuce 17 ba.

Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan wani mutum mai shekaru 26 bisa laifin da ta tabbatar ya aikata a lokacin yana karami.

Hukumomin Saudiyya sun zartar da hukuncin kan Mustafa al-Darwish a ranar Talata, kan laifin da kungiyoyin kare hakkin bil Adama suka ce ana zargin ya aikata lokacin da shekarunsa na haihuwa basu wuce 17 ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya wanda ya tabbatar da zartar da hukuncin, ya ruwaito cewa an samu Al-Darwish da hannu a zanga-zangar nuna adawa da gwamnati da zummar kashe jami’an tsaro a tsakanin shekarar 2011 da 2012.

Tun a shekarar 2015 aka kama matashin wanda mabiyin mazhabar Shi’a ne kan zargin kitsa zanga-zangar ta’addanci kuma aka zartar masa da hukuncin kisa a shekarar 2018, inda a watan Mayun bana wa’adin daukarar kararsa ya kare.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yanke wa matashin hukuncin ne duk da tabbacin da kasar ta bayar a bara cewa za a daina yanke wa kananan yara hukuncin kisa.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International, ta ce babu adalci a shari’ar yayin da danginsa suka ce ya janye amsa laifin da ya yi a baya kasancewar ya amsa laifin ne saboda azabtar da shi da aka yi.

“Sai kawai a kafafen watsa labarai na Intanet muka ji cewa an zartar da hukuncin a ranar Talata,” a cewar ’yan uwansa.

Kazalika, ’yan uwansa sun ce an yanke masa wannan hukuncin ne kawai saboda wani hoto da aka gani a wayarsa da ya ci zarafin wani jami’in tsaron Saudiyya.