✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saudiyya ta ki hukunta Ronaldo kan zama da budurwa babu aure

Laifi ne a Saudiyya mace da namijin da ba muharraminta ko mijinta ba su rika zama tare

Saudiyya ta dauke kai kan dokar hukunta masoyan da ke zama tare babu aure kan dan wasan kwallon kafar duniya Cristiano Ronaldo da budurwarsa Georgina Rodriguez.

Laifi ne a Saudiyya mace da namijin da ba muharraminta ko mijinta ba su rika zama tare, sai dai kafafen yada labaran kasar sun rawaito cewa, alamu kasar ta sassauta dokar a kan Ronaldo da budurwar tasa.

Ronaldo ya koma kungiyar kwallon kafar Al-Nassr da ke Saudiyya ne bayan soke kwantiraginsa da kulob din Manchester United da ke Birtaniya ya yi.

Manchester United ta raba gari da dan wasan ne bayan wata hirarsa da ta tayar da kura a watan Nuwamba, wadda a ciki ya caccaki shugabannin kungiyar.

Bayan dawowarsa Saudiyya, dan wasan ya bayyana wa manema labarai cewa ya zabi komawa kungiyar Al-Nassr ne son taimaka wa ci gaban harkar kwallon kafa a yankin Larabawa da kuma zamowa abin koyi ga ’yan wasa da ke tasowa.