✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta mayar da Sallar dare zuwa minti 30

Gwamnatin Saudiyya, ta umarci masallatan cikin unguwanni da su rika kammala Sallar Isha da Taraweeh cikin minti 30.

Ministan Harkokin Addinin Musulunci a Kasar Saudiyya, Sheikh Abdullatif Al-Sheikh ya ba da umarnin tsakaita tsawon Sallar Taraweeh a masallatan cikin unguwanni a kasar zuwa minti 30 a watan Ramadan.

Hakan na dauke ne cikin sanarwar da ministan ya aike wa masu ruwa da tsaki da limaman masallatan kasar don yaki da cutar coronavirus a ranar Lahadi.

Sanarwar, ta ce sallar za a rika yin Sallar Isha da ta Taraweeh din ne, a kuma a kammala su ne a cikin mintoci 30, don rage tsawon taruwar jama’a domin rage cunkoso a masallatai.

Kazalika, sanarwar, ta ce dole ne limamai a dukkannin masallatai su bi sabuwar dokar don kammala ibada cikin watan Ramadan lafiya.

Ma’aikatar, ta kuma umarci ma’aikatan masallatai da su kasance cikin sabon shirin samar da sabbin shimfidun sallah daga lokaci zuwa lokaci, tabbatar da sanya takunkumi, da kuma bayar da taraza a tsakanin masallata