✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saudiyya ta sake bude wuraren shan gahawa da shisha

Da farko kasar ta rufe gidajen abinci da gahawa da nufin rage yaduwar cutar COVID-19.

Tun bayan tsanantar cutar COVID-19, kasar Saudiyya ta rufe wuraren taruwar mutane ciki har da wuraren shan shisha a kasar.

Sai dai, a wannan karon gwamnatin kasar ta amince a sha shisha a wuraren shan gahawa a fadin kasar, daga ranar Litinin mai zuwa, bayan da aka sassauta dokar COVID-19.

Ma’aikatar kula da birane da karkara ta amince a sayar da shisha ga wadanda aka yi wa rigakafin cutar, kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar, SPA, ya ruwaito.

Yayain da za a rika shan shishar a sarari a wuraren shan gahawa, an haramta sha a wuraren cin abinci.

Tun asali, Saudiyya ta rufe gidajen cin abinci da shan gahawa; wadanda yawanci a nan ake shan shisha, a wani mataki na rage tasirin cutar.