✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta bukaci mahajjata su jinkirta shiri

Kasar Saudiya ta bukaci maniyatta Hajjin bana da su jinkirta biyan kudin kujera saboda rashin tabbas game da annobar coronavirus. Ministan Aikin Hajji na kasar…

Kasar Saudiya ta bukaci maniyatta Hajjin bana da su jinkirta biyan kudin kujera saboda rashin tabbas game da annobar coronavirus.

Ministan Aikin Hajji na kasar Saudiyya Muhammad Banten ne ya sanar da hakan ta gidan talabijin na kasar, inda ya bukaci maniyatan hajjin na bana su dan saurara a ga abin da halin zai yi.

Muhammad Banten, ya jaddada cewa Saudiya na bai wa lafiyar mahajjata da na ‘yan kasarta mahimmanci dan haka take daukan matakan kare su daga cutar Coronavirus.

“Saudiyya a shirye take ta dauki nauyin mahajjata da masu yin Umara”, kamar yadda Ministan ya shaida wa gidan talabijin na Al-Akhbariyya, “amma a halin da ake ciki yanzu, muna magana ne a kan annobar da ta addabi duniya… Masarautar Saudiyya ta damu da kare lafiyar Musulmi da ‘yan kasa, saboda haka muka bukaci ‘yan uwanmu Musulmi a dukkan kaashen duniya su dan dakata kafin su kashe magana game da zuwa Hajji har sai an dan samu haske”.

Tun bayan barkewar annobar coronavirus kasar ta Saudiyya ta dakatar da aikin Umara kana ta dauki matakan rufe manyan masallatai masu alfarma na kasar wato Masallacin Makka da na Madina sannan ta hana shige da fice a babban birnin kasar, Riyadh.

Ana sa ran mutum sama da miliyan biyu ne za su yi aikin Hajji a bana a watannin Yuli da Agusta.

Aikin Hajjin dai daya ne daga cikin shikashikan Musulunci wanda ya wajaba a kan Musulmin da ke da hali ya yi akalla sau guda a rayuwarsa.

Mutane 1,563 ne suka kamu da cutar coronavirus yayin da mutum 10 suka mutu a sakamakon cutar a kasar Saudiya.