✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta yi wa musulmi albishir kan aikin Umarah

Mun dauki dukkan matakan kariya da tabbatar da ganin an samar da tazara a tsakanin maniyyata.

Tashar zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa ta Sarki Abdulaziz da ke birnin Jidda, ta fara shirye-shiryenta na karbar maniyyatan aikin Umarah daga ko ina a sassan duniya.

Da yake bayani a garin Okaz da ke Kasar Saudiyya, Shugaban kamfanin dake kula da al’amuran da suka shafi aikin Hajji da Umarah a tashar jirgin sama ta Jidda, Injiniya Adnan Al-Saqqaf, ya bayyana cewa dukkan shirye-shirye sun kammala don fara karbar maniyyatan Umarah a tashar jirgin ta Jidda.

Adnan ya ce tuni sun dauki dukkan matakan da suka kamata don kare kai daga yaduwar cutar coronavirus.

“Mun dauki dukkan matakan kariya da tabbatar da ganin an samar da tazara a tsakanin maniyyata a wurin da aka ware don karbar baki daga kasashen duniya a tashar ta Jidda.”

“Ma’aikanmu a shirye suke tsaf don tunkarar wannan aiki duk da cewa zamu raba maniyyatan zuwa rukuni-rukuni ta yadda zamu rinka kara adadin maniyyatan a hankali.”

Al-Saqqaf ya ce sun yi shirin raba hanyar shiga da fita da maniyyata za su rinka bi, wanda yanzu haka suna daf da kammala wannan aikin nan bada jima wa ba, kuma suna sa ran fara karbar maniyyata zuwa mako mai zuwa.