✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta zartar wa mutum 81 hukuncin kisa

Daga cikin adadin, mutum 73 ’yan asalin kasar ta Saudiyya ne, bakwai ’yan Yemen

Kasar Saudiyya a ranar Asabar ta sanar da zartar wa da mutum 81 hukuncin kisa, bayan kotuna sun tabbatar da laifukan da ake zarginsu da aikatawa.

Wannan dai shi ne adadi mafi yawa da kasar ta taba zartar wa hukunci a cikin ’yan shekarun nan.

Ko a shekarar 2020 dai sai da kasar ta zartarwa mutum 27 hukuncin, a 2021 kuma ta zartar da shi a kan mutum 67.

Kafin wannan adadin, rabon da a zartarwa mutane masu yawa hukunci irin haka tun a 1980, in ban da a 2016 da aka kashe mutum 47.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya (SPA), an zartar wa mutanen hukuncin ne bayan an same su da aikata ayyukan ta’addanci da kuma sauran manyan laifuka.

Kamfanin ya ce mutanen sun hada da mambobin kungiyoyin Al-Ka’ida da ISIS da kuma masu goyon bayan  ’yan tawayen Houthi na Yemen.

Daga cikin mutum 81 da aka kashe, 73 ’yan asalin kasar ta Saudiyya ne, bakwai ’yan Yemen da kuma mutum daya dan kasar Siriya.

“Laifukan da suka aikata sun hada da zama mambobin kungiyoyin ta’addanci irin su ISIS da Al-Ka’ida da Houthi, masu neman kai wa mazauna Saudiyya hari da kuma tsallakawa kasashe masu fama da rikici don shiga ta’addanci,” inji kamfanin, kamar yadda ya ambato wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya.

Sauran laifuka da aka tabbatar mutanen sun aikata sun hada da yin garkuwa da mutane, azabtarwa, aikata fyade, safarar makamai da kuma bama-bamai zuwa cikin kasar.

“Kasarmu za ta ci gaba da daukar tsauraran matakai a kan ayyukan ta’addanci da ’yan ta’addan da ke barazana ga duniya baki daya,” inji SPA.