✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya za ta bude zirga-zirgar jirage ranar Talata

Kasar Saudiyya za ta bude sufurin jirage na kasa da kasa daga ranar Talata, watanni shida bayan zaman dar-dar kan annobar COVID-19. Masarautar ta ce…

Kasar Saudiyya za ta bude sufurin jirage na kasa da kasa daga ranar Talata, watanni shida bayan zaman dar-dar kan annobar COVID-19.

Masarautar ta ce daga ranar Talata za a fara barin jam’ian gwamnati da dalibai da masu neman lafiya da kuma sojoji su rika yin shige da fice.

Wadanda ba cikakkun ‘yan kasar ba za su samu damar shiga kasar daga ranar Talata idan har ba a same su da cutar coronavirus ba, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ya fitar.

Sai dai ta ce “bayan 1 ga watan Janairu shekara mai zuwa” sauran ‘yan kasar za su fara fita waje kuma za ta bayyana ainahin lokacin budewar cikin Disemba.

Saudiyya ta hana zirga-zirgar jirage tun a watan Maris, wanda hakan ya sa ‘yan kasarta da ke kasashen waje kasa dawowa gida.

Ziyarar Umraha 

Gwamnatin kasar ta ce za ta sanar da ranar da za ta bude ziyarar Umrah a kasar.

Saudiyya ta soke ziyarar Umrah ce a watan Maris saboda tsoron yaduwar annobar COVID-19 a kasarta mai tsarki.

A watan Yuni kasar ta rage mutane da za su haharci aikin Hajji 2020 zuwa mutum 10,000 kacal sabanin mutum miliyan biyu da rabi da suka yi hajji shekarar da ta gabata.

Gwamnatin kasar ta yi kokarin hana yaduwar cutar da aka samu fiye da mutum 325,000 sun kamu, yayin da fiye da mutum 4,200 suka mutu.

A watan Yuni, gwamnatin ta dage dokar da ta saka a kasar kan kasuwanci da gidajen sinima da sauran wuraren bukukuwa.