✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya za ta dauki nauyin raba jariran da aka haifa manne da juna a Kano 

Za a tafi da yaran Saudiyya ranar Alhamis, din yi musu aiki a can

Kasar Saudiyya za ta dauki nauyin yin aiki don raba wasu jarirai biyu ’yan asalin jihar Kano da aka haifa a manne da juna.

Ofishin jakadancin kasar da ke Kano a wata sanarwa da Kakakinsu, Ahmad Idris Yunus, ya fitar ranar Talata ya ce Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulazeez ne ya ba da umarnin daukar nauyin aikin nasu.

Sanarwar ta ce labarin ’yan biyun ya ja hankalin hukumomin kasar ne tun wata biyu da suka gabata. Hakan ya sa suka fara bin hanyoyi da ka’idoji domin taimaka wa ta hannun wata gidauniya da ke karkashin kulawar Sarki Salman.

A cewarsu, “Muna da labarin yadda ’yan biyun suka shafe a kalla wata bakwai zuwa takwas a babban asibitin kasa da ke Abuja amma ba su samu damar ayi musu aikin ba sakamakon rashin kudi.

“Kazalika, duba da yanayin yaran, Shugaban ofishin jakadancin Saudiyya da ke Kano, Khalil Ahmad Admawi, ya dauki gabarar bin hanyoyin da za a fitar da su zuwa kasar Saudiyya tare da gudunmawar Asibitin koyarwa na Muhammadu Abdullahi Wase da ke Kano,” inji sanarwar.

Ofishin jakadancin ya ce abin damuwa ne yadda yaran tare da mahaifansu suka shafe sama da wata guda a asibitin kafin su samu tallafi.

Ana sa ran ’yan biyun za su bar Abuja ranar Laraba zuwa Kano, inda daga bisani za su kama hanyar zuwa kasar ta Saudiyya ranar Alhamis.