✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya za ta raba rigakafin COVID-19 kyauta

Kasar ta Saudiyya na da burin raba rigakafin COVID-19 din kyauta ga jama'ar kasar

A wata tattauna wa da Ma’aikatar Lafiya ta kasar Saudiyya ta yi da Gidan Talibijin na Al-Ekhabariya, ta sanar da cewa za ta samar da wadaccen maganin rigakafin COVID-19 a kasar kuma za a raba rigakafin kyauta ga dukkan ’yan kasar.

Mataimakin Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta kasar, Dokta Abdullah Al-Asiri ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai da aka saba gudanar wa kowace rana kan annobar Coronavirus a kasar.

A cewarsa, “Saudiyya ta dauki nauyin rarrabawa jama’ar kasar rigakafin kyauta duk da kasar ba ta a cikin kasashen da suka samar da rigakafin.”

Al-Asiri ya ce, suna sa ran akalla kashi 70 cikin 100 na jama’ar kasar za su amfana da rabon rigakafin kyauta daga yanzu zuwa karshen shekarar 2021.

Kazalika, Al-Asiri ya bayyana ce wa, kasar ta Saudiyya na cikin kasashe ashirin na G20, masu karfin tattalin arziki a duniya da suka fara daukar matakan kariya da samar da rigakafin kyauta ga mutanen da suka kamu da cutar.

A wani labarin kuma, Jami’in Hulda da Al’umma na Ma’aikatar Lafiya a kasar ta Saudiyya Dokta Mohamed Al-Abdel Alil, ya bayyana ce wa, kasar za ta karbi rigakafin ta Coronavirus kuma za ta rarrabawa jama’ar kasar kyauta.

Mohamed Al-Abdel Ali, ya bayyana haka a ranar litinin, inda ya shaida wa manema labarai ce wa, a makon da ya gabata adadin mutanen da suke kamuwa da cutar Coronavirus a kasar ya ragu da kaso 6.3 cikin dari.

Ya kuma bukaci jama’ar da su kara kiyaye wa sosai wurin daukar matakan kariya da dakile yaduwar COVID-19 kamar yadda hukumomin lafiya suka gindaya.

Aminiya ta ruwaito cewa, Kamfanin Pfizer na Amurka da ya jagoranci kirkiro rigakafin cutar Coronavirus, ya ce zai samar da rigakafin guda miliyan 50 kafin karshen 2020, da kuma guda biliyan 1.3 zuwa karshen shekarar 2021.