✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saura kiris tumatir ya yi tashin gwauron zabo

Rufe madatsar ruwa ta Tiga ta sa manoman tumatir kaura, saboda rashin ruwan da za su yi ban

Manoman tumatir a Jihar Kano sun ce nan gaban farashinsa zai yi tashin gwauron zabo saboda rufe Madatsar Ruta ta Tija da ke samar musu da ruwa domin noman rani.

Manoman sun ce tun bayan da aka rufe madatsar ruwan a ranar 1 ga watan Nuwamban 2021 — ake kuma sa ran sake budewa a ranar 31 ga watan Maris — harkokinsu noman rani suka ja baya, dole wadansu suka bar gonakinsu ba su noma ba, saboda rashin ruwa.

Aminiya Ta gano cewa yawancin manoman tumatir na rani sun koma wadansu wuraren da ke kusa da ruwa domin ci gaba da harkokin; Duk da hakan, tsugune ba ata kare ba, saboda hatta wadanda suka samu gonaki, sun yi musu kadan.

Wani mai sayar da kayan lambu a Kasuwar Kayan Gwari ta ’Yan Kaba a Kano, Mansur Bello Seemon, ya ce a halin yanzu ana kawo musu tumatir ne daga Zariya da wasu sassan jihohin Katsina da Kano.

Binciken da wakilinmu ya gudanar a kasuwanni ya nuna yanzu haka ana sayar da babban kwandon turmatir N10,300, sabanin farashinsa na N3,100 a irin wannan lokaci a bara.

“Bara ko’ina ka a kasuwar nan tumatir ne, amma tun da aka rufe Madatsar Ruwa ta Tiga muka koma sayowa daga Katsina da Zariya.

“Yanzu babban kwandonsa N10,200 ne kuma bisa dukkan alamu tumatir zai yi tsada matuka a bana,” inji Seemon.

Rahotanni sun nuna rashin ruwan noman rani ya sa manoma da ke aiki a filin noman rani na Kadawa mai fidin kadada 22,o00 sun yi kaura.

Wasu daga cikinsu sun koma wuraren da ke da kusanci da ruwa a gabar Kogin Kano domin ci gaba da noman tumatir.

Shugaban Kungiyar Manoman Tumatir ta Najeiya (TOGAN), Alhaji Sani Danladi Yadakwari, ya ce gonakin da manona suka noma a Kadawa ba su kai kashi 10 cikin 100 na gonankinsu ba, a sakamakon rufe Madatsar Ruwar ta Tiga.

Ya ce manoman na cikin tsaka mai wuya, wanda ke iya haifar da karancin tumatir da kuma tsadarsa.

“A sakamakon rufe madatsar, wasu mambobinmu sun kowa wuraren da ke kusa da ruwa domin ci gaba da noman tumatir, amma bai kai abin da aka noma a filin Kadawa bai kai kashi 10 cikin 100 da abin da aka noma a bara ba,” inji Yadakwari.

Shi ma wani manomin na tumatir, Malam Abdullahi Garba, ya ce shi da yawancin takwarorinsa ba su yi noma ba a bana.

Ya ce rufe madatsar ta sa sun kasa samun inda za su noma, saboda haka sai dai jama’a su yi hakuri, domin bisa dukkan alama zai yi tsada nan gaba.

A nata bangaren, Hukumar Kula da Kogin Hadejia Jama’are (HJRBDA) da ke da alhalin kula da madatsar, ta bayyana cewa rufewar ta zama dole, domin tana matukar bukatar gyara.

Kakakin hukumar, Salisu Baba Hamza ya akwai kwararan dalilan da rufe madatsar ruwan gaba daya.