✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sauya fasalin Kudi: Yadda darajar Naira ke ci gaba da faduwa warwas

A yanzu dala daya ta haura Naira 800 a kasuwar bayan fage.

Darajar Naira na ci gaba da faduwa yayin da farashin Dala a kasuwar bayan fage ya kai Naira 818 a ranar Litinin.

Binciken Daily Trust ya nuna cewa faduwar darajar Naira bai rasa nasaba da sanarwar da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar na sauya fasalin kudin wanda za a kaddamar daga ranar 15 ga watan Disamba 2022.

Bayan wannan sanarwa a makon da ya gabata, darajar Naira ta soma faduwa daga yadda ake canjar Dala daya a a kan N765 zuwa N818 a ranar Litinin, kuma da alama faduwar ba ta tsaya nan ba.

Aminiya ta ziyarci kasuwar ‘yan canji da ke Unguwar Zone 4 a Abuja, ta kuma ruwaito yadda mutane da yawa suke sintirin neman Dalar, amma ta yi wahala.

Wakilinmu da ya zaga wurin wasu ‘yan canjin a matsayin mai saye, ya ce yana son $10,000, amma babu wani mai canjin da ya ke da wannan adadin da zai sayar, wasu cewa su ka yi ba su da ko $5,000.

Wani dan canji mai suna Isma’ila Yusuf ya bayyana cewa, Dala na matukar wahala, kuma ba da dadewa ba jami’an EFCC su ka zo kamen wadanda suka zo sayen Dalar mai yawa.

Sai dai ya ce, ‘yan canjin na taka tsantsan wajen sayar da Dalar mai yawa ga mutane a yanzu.

Kawo yanzu dai ba a iya tabbatar da musabbabin karancin dalar, inda ake zargin boyeta ‘yan canji suke yi domin cin kazamar riba, ko kuma da gaske karancinta ake yi.

Karancin masu sayar da Dala

Wani dan canji da wakilinmu ya yi hira da shi, ya ce, yanzu da wuya ka ga mutum zo ya same su da Dala ta sayarwa, hakan kuma ya taimaka wa karancinta.

Sannan wasu manyan ‘yan siyasa har gida su ke gayyatar ‘yan canji, domin su sayar musu da Dalar don kaucewa sa idon EFCC .

A wani binciken da Aminiya ta yi a kasuwar bayan fage ta ‘yan canji a Legas, ana sayen Dalar kan N790 zuwa N800, sannan a sayar da ita a tsakanin N795 zuwa N805.

Wani mai suna Alhaji Abdullahi a hirar sa da wakilinmu, ya ce zai iya sayen Dalar a kan N807 idan yawanta ya kai $4000.

Kokarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin shugaban kungiyar ‘yan canji na ABCON kan faduwar darajar Nairan ya faskara, saboda sun ki su ce uffan kan batun.

CBN ya haramta sayar da kudaden ketare

Idan za a iya tunawa, a cikin watan Yuli 2021 ne CBN ya hana sayarwa da kamfanoni kudaden ketare a duk fadin kasar nan.

Bankin ya ce, ana amfani da ‘yan kasuwar bayan fagen wajen zurare kudin musayar kasar ta barauniyar hanya da kuma aikata rashawa.