✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Sauya Shugabannin Tsaro bukata ce da ta zama tilas’

Manyan hafsoshin tsaron Najeriya sun gaza, ba su da wani uzuri.

A ranar Litinin wani tsohon Darakta Janar na Hukumar Jami’an Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Mike Ejiofor, ya nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya ba ’yan Najeriya mamaki a shekarar 2021 ta hanyar sauya dukkanin manyan hafsoshin tsaro a yayin da matsalolin tsaro ke ci gaba da ta’azzara a fadin kasar.

Ejiofor, yayin wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels, ya bayyana cewa babu wani ci gaba da za a samu a yaki da matsalolin tsaro musamman ta’addanci, fashi da makami, da kuma garkuwa da mutane matukar ba a sauya salo da dabarun tunkarar lamarin ba.

Tsohon Shugaban na DSS ya ce, “Ina sa ran cewa Shugaban Kasar zai ba ’yan Najeriya mamaki, ya sauya manyan hafsoshin tsaro wand hakan ne zai sa ’yan Najeriya su sauya halayensu game da lamarin tsaro a kasar.”

“Ina ganin ta hanyar sauya salo da dabaru, samar da ingatattun kayan aki, da kuma dabi’un jami’an tsaro, za mu samu ci gaba wanda babu shakka ina da yakini a kan hakan.”

Aminiya ta ruwaito cewa wannan kira ba shi ne farau ba daga bangarori da dama ciki har da Majalisar Dokoki ta Tarayya, inda ake kwankwashen ganin Shugaba Buhari ya sauya manyan hafsoshin tsaron kasar.

A Juma’ar makon jiya ce bayan Daliban Sakandiren Kimiyya da ke garin Kankara sun kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane, Shugaba Buhari ya nuna alamun zai sauya manyan hafsoshin tsaron kasar.

Shugaba Buhari ya ce bai gamsu da ayyukan da sojoji da sauran jami’an tsaro ke yi wajen tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar al’umma duba da yadda kwazon da suke yi bai haifar da wani da mai ido ba.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne fadar Gwamnatin Jihar Katsina, a yayin da yake gabatar da jawabai ga daliban 344 da suka shafe kwanaki bakwai a hannun wadanda suka yi garkuwa da su.