✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sauya tsarin Najeriya kadai ba zai wadatar ba —Jonathan

Najeriya ba za ta gyaru ba sai mun gyara halayenmu, inji shi

Tsoshon Shugaban Kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce sauya tsarin Najeriya bai zai wadatarba wajen magance matsalolin da ke addabar kasar.

Jonathan, wanda ya jagornaci taron Taron Tattaunawar Daily Trust karo na 18 a Abuja ranar Alhamis; ya ce dole sai Najeriya ta magance matsalolin da suka dabaibaye ta kafin al’amuranta su tafi daidai.

“Tattaunawar sauya fasalin kasa ba zai amfane mu ba, har sai mun gyara zukatanmu.

“Wasu daga cikin matsalolin da ake fama da su a matakin kasa na nan ana fama da su matakin jihohi da kananan hukumomi…wani lokaci ma har a matakin al’umma,” inji shi.

Taken taron wanda shi ne karo na 18 shi ne: “Sauya tsari: Me ya sa? kuma ta Yaya?”.

Jonathan ya bayyana cewa ’yan Najeriya na fama da rashin yarda da juna, matsalar da ya ce wajibi ne a kawar muddin kasar na so ta ci gaba.

“Ba za mu sauya tsarin Najeriya ba tare magance matsalolin da suka raba kanmu ba; fadanci, bambancin addini da rashin kishin kasa,” inji shi.

‘Ba sabon abu ba ne’

Ya ce batun sauyin tsarin Najeriya ba bakon abu ba ne domin tun bayan samun ’yanci ’yan Najeriya ke kiraye-kiraye da a yi.

Jonathan ya ce  hakan ce ta sa Gwamnatin Janar Yakubu Gowan aka sauya tsarin Najeriya daga yankuna zuwa jihohin 12.

“Babban mataki ne na kubutar da kasar daga watsewa bayan an gama yakin basasa.”