✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sauye-sauyen da Ronaldo ya kawo a Manchester United

A duk lokacin da ake bukatar taimakonsa, za ka gan shi da karfinsa.

A farkon kakar bana ce Cristiano Ronaldo ya dawo Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United bayan ya bar kungiyar a shekarar 2009 zuwa Kungiyar Real Madrid.

Dan wasan ya samu nasarori da yawa a kungiyar, inda ya lashe kofuna 15 ciki har da Zakarun Turai da sauransu, sannan ya lashe Gwarzon Dan Kwallo sau hudu.

Daga Madrid ya koma Kungiyar Juventus, inda ya lashe wasu kofunan guda biyar.

Bayan dawowarsa Manchester United, dan wasan ya fara da kafar dama, inda a wasansa na farko ya zura kwallo a raga.

Sai dai duk da cewa yana zura kwallo a raga, Kungiyar ta Manchester United tana ta fama da matsalar kwan-gaba-kwan-baya, inda hakan ya sa wadansu magoya bayan kungiyar suke cewa dawowarsa ce ta kawo matsalar.

Da yawa daga cikin magoya bayan kungiyar sun fi yin kira da a kori mai horar da ’yan wasan, Ole Gunnar Solskjær, inda suke cewa kungiyar tana da zaratan ’yan wasa da ake bukata domin ciyar da duk wata kungiya gaba, amma bai san yadda zai yi da su ba, kuma a ganinsu hakan ya sa ba ya samar da nasarar da ake bukata.

Duk da wadansu suna ganin laifin kocin, wadansu suna ganin cewa dawowar Ronaldo ta sa ’yan wasan kungiyar da dama da suka rika daukar nauyin kungiyar a kakar bara sun ja da baya.

Misali Bruno Fernandes, wanda a kakar bara ya zura kwallo 27, idan magoya bayan kungiyar suka yi tunanin zai dora a bana, amma sai lamarin ya koma baya da sauran misalai da ake bayarwa.

Sai dai kuma a wasan kungiyar na Zakarun Turai a ranar Talatar da ta gabata, Ronaldo ya zura kwallo biyu a ragar Atalanta, wanda hakan ya sa aka tashi wasan 2-2 bayan Atalanta ta yi yunkurin doke Manchester United.

Da Atalanta ta doke Man United, da ta kara jefa kungiyar a cikin wani sabon tashin hankali, bayan dan sauki da aka samu bayan doke Kungiyar Tottenham da ci 3-0 a daidai fara kirayekirayen a sallami kocin kungiyar, Solskjær.

Tsohon dan wasan Manchester United Rio Ferdinand cewa ya yi a game da wasan, “Me kuma kuke so a fada game da wannan dan wasan Cristiano Ronaldo.

A duk lokacin da ake bukatar taimakonsa, za ka gan shi da karfinsa.”

Shi ma Solskjær da yake jawabi bayan wasan, ya kwatanta Cristiano Ronaldo da Michael Jordan na wasan kwallon Kwando a kungiyar wasan kwallon Kwando ta Chicago Bulls.

Duk da cewa dawowar Ronaldo ta sa kocin yana shiga rudu wajen zabo ’yan wasa 11 da za su fara wasa, hakan zai nuna cewa dawowarsa ba ta zama matsala ba, kasancewar daga dawowarsa zuwa yanzu, shi ne ya rika ceto kungiyar a wasanni masu muhimmanci kuma a duk lokacin da aka fi bukatar hakan.

Daga cikin matsalolin da ake samu akwai matsalar ’yan wasan bayan kungiyar, inda ake yawan samun kananan kura-kurai.

Daga dawowarsa zuwa yanzu, ya zura kwallo 9, sannan za a iya cewa ya kawo karin kwarjini ga kungiyar, inda a yanzu duk girman kungiya, za ta rika kaffakaffar da kasancewarsa a fili.