✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sauyin Yanayi: Manyan kasashe za su tallafawa matalauta

Masu rajin kare muhalli na ganin akwai sauran rina a kaba.

An karkare taron COP27 tare da cimma matsaya na ganin an taimaka wa kasashen da suka tafka asara a sakamakon matsalar sauyin yanayi da kudi.

Mahalartar taron sauyin yanayi sun cimma matsaya na samar da kudade don tallafa wa kasashen da suka fi tafka asarar a sakamakon matsalar da sauyin yanayin ta haifar musu.

An kai matakin ne dai a taron da aka fi sani da COP 27 da ya gudana a wurin shakatawa na Sharm el Sheikh da ke kasar Masar.

Wannan batu na rage wa kasashe matalauta radadin asarar, ya sa an tsawaita taron da aka saba yi na mako biyu da kwana guda.

A yayin da ake kallon hakan a matsayin ci gaba, su kuwa masu rajin kare muhalli na ganin akwai sauran rina a kaba, ganin taron bai kai ga cimma matsaya a yarjejeniyar rage yawan hayakin da ke gurbata iska da manyan kasashen duniya suka fi fitarwa ba, wanda kuma shi ne tushen matsalar da ke haifar da matsalolin na sauyin yanayi.