✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Sayar da masarar gashi ta yi min komai a rayuwa’

Ya shawarci mutane da kar su raina sana’a domin duk sana’a tana da rufin asiri komai kankantarta.

Ibrahim Amadu Oga, ya kwashe fiye da shekara 30 yana sayar da masarar gashi, sana’ar da ya ce ta taimaki rayuwarsa kuma yana alfahari da ita.

Ya shaida wa Aminiya cewa ya fara sana’ar tun kafin ya yi auren fari, a lokacin suna sayen gonar masara daya a kan Naira 800, har ga shi a yanzu suna saya Naira 250,000 zuwa N300,00o.

Oga Ibrahim wanda ke zaune a Unguwar Jabba a Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna, ya ce da sana’ar ya auri har mata uku, ya kuma mallaki gidanda yake zaune da iyalansa cikin kwanciyar hankali.

Ya ci gaba da cewa, “Idan muka sai gonar masara, a gona to akwai masu bin mu zuwa gonakin don a kasa musu su saya a can, abin da ya yi saura kuma sai mu kwashe mu kai kasuwanni mu sayar.

“Kuma tun lokacin da na fara wannan sana’ar, lokacin daya ne muka taba fuskantar matsala a lokacin hawa gwamnatin Shugaba Buhari na farko, ya hana sana’ar gashin masara.

“Toh a wannan lokacin mun yi asara sosai na gonakin masaran da muka saya, shi ne kawai abin da zan iya tunawa na wahalar da na san mun sha.”

Ya shawarci mutane da kar su raina sana’a kowace iri, domin duk sana’a tana da rufin asiri komai kankantarta.

Wakilinmu ya iske mutane maza da mata da dama a gonar sun je sayen masara, kuma wadanda Aminiya ta tattauna da su sun yi bayani cewa suna sami rufin asiri da sana’ar.

Lami Sabo wadda ke sana’ar gasa masara a kofar Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, ta ce ta kusa shekara 20 tana sana’ar gasa masara.

“Da lamari da sauki ba kamar yanzu ba; ka ga dai ga kudin mota daga Samaru zuwa nan na kashe Naira 600, kuma masara ana ba mu uku ne a kan Naira 100, kuma babu zabi hada maka ake yi da babba da karami da mai ido da mara ido.

“Sannan ga kudin gawayi akalla ka sai na Naira 300; mu kuma mukan sayar da kowane daya a kan Naira 50.