Sayen kuri’a ya haddasa rikici a Bichi jihar Kano | Aminiya

Sayen kuri’a ya haddasa rikici a Bichi jihar Kano

    Daga Lubabatu I. Garba Kano

An samu barkewar rikici a mazabar cikin garin Bichi jihar Kano sakamakon wasu matasa daga wata jam’iyya suka rika rarrabawa masu zabe kudi da niyyar sayen kuri`arsu.

A daidai lokacin da matasan suke wannan aiki na rabon kudin sai wasu magoya bayan wata jam’iyyar suka dauko kyamara suna daukar hoton abin da ke faruwa hakan ya sa wani daga cikin wadanda ake daukar hoton nasu ya taso ya kwace kyamarar ya tattaka ta a kasa.

Wannan abu ya sa rikici ya barke a tsakanin magoya bayan jam’iyyun. Wanda kuma ya jawo aka shiga ba hammata iska tare da yayyaga wa juna riguna.

Wannan rikici ya jawo an sami tsaikon gudanar da zabe na wani dan lokaci, har sai da jami`an tsaro suka shawo kan rikicin.