✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sean Dyche ya zama sabon kocin Everton

Lampard ya bar kungiyar a mataki na 19 a teburin Firimiyar Ingila.

Sean Dyche ya zama sabon kociyan Everton bayan kwanaki da kungiyar ta raba gari da Frank Lampard.

Goal ta ruwaito cewa Sean Dyche ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu da rabi da kungiyar da ke Arewacin Liverpool.

Dyche ya maye gurbin Frank Lampard wanda kungiyar ta sallama a makon jiya bayan West Ham ta doke ta ci biyu da nema.

Lampard ya bar kungiyar a mataki na 19 a teburin Firimiyar Ingila da tazarar kwallaye tsakaninta da Southampton da ke karshen teburin.

Yayin da ya rage wasanni takwas a karkare kakar wasannin da ta gabata ce, Burnley ta raba gari da Sean Dyche bayan ya shafe shekaru 10 yana jan ragamar horas da ’yan wasan kungiyar.

Burnley ta yanke shawarar sallamar Dyche ne bayan ta tabbatar da cewa ta yi sallama da gasar Firimiyar Ingila, inda yanzu haka take buga gasar Championship ta ’yan dagaji.

Sai dai duk da haka Dyche ya kafa tarihi a Burnley wadda ya kai har zuwa zagayen buga wasannin neman gurbi a gasar Europa, sannan kuma ta shafe kakar wasannin shida a jere tana fafatawa a Firimiyar Ingila.

A halin yanzu dai Everton za ta jarraba sa’arta da sabon kociyan, wadda wasanni uku kacal ta yi nasara cikin dukkanin wasannin da ta buga a bana.