✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

SEMA ta tallafa wa mutum 150 a Nguru

Wannan tallafi zai rage musu radadin halin da suka shiga.

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), ta rarraba kayayyakin tallafi ga fiye da mutum 150 da iftila’i na guguwa ya shafa a Karamar Hukumar Nguru.

Wannan na zuwa ne bayan umurnin da Gwamna Mai Mala Buni na Jihar ya bai wa Hukumar na samar da kayayyakin agaji ga wadanda bala’in ya auku a kansu.

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, Gwamnan ya umarci Hukumar da ta zakulo masu karamin karfi da wadanda ke da matsananciyar bukatar taimako domin cin moriyar tallafin.

A cewar Babban Sakataren SEMA, Dokta Muhammad Goje, “Bayan kokarin da ake yi na tabbatar da tallafin ya isa garesu, ana kuma kokarin ganin an sama musu sauran abubuwan walwala da sauran nakasassu a fadin Jihar.

“Wannan tallafi zai dan taba zuciyar wadanda guguwar ta shafa su samu abin da za su rage radadi domin ci gaba da rayuwa cikin nutsuwa tare da iyalan su.

“Hakan zai kuma karfafa musu gwiwa na fita su fafata wajen nemo abin da za su gyara gidajen su,” a cewarsa.

A nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Nguru, ya yi godiya ga Gwamna Buni kan yadda ya taimaka musu cikin kankanin lokaci bayan faruwar lamarin bisa la’akari da halin da suka tsinci kansu a ciki.