✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Senegal ta kai wasan karshe a gasar AFCON

Senegal ta samu nasara bayan ta lallasa tawagar Burkina Faso.

Tawagar kwallon kafar kasar Senegal ta kai wasan karshe a gasar Kofin Nahiyyar Afirka ta AFCON 2021 da ke gudana a Kamaru.

Senegal ta samu nasara ne bayan ta lallasa tawagar Burkina Faso a wasan daf da na karshe da suka barje gumi a yammacin Laraba.

A wasan da aka fafata a filin wasanni na Ahmadou Ahidjo da ke Younde, babban birnin Kamaru, Senegal ce ta jefa kwallaye uku yayin da Burkina Faso ta samu nasarar farke daya kacal, lamarin da ya sanya aka tashi wasan 3-1.

Abdou Diallo ne ya jefa wa Senegal kwallon farko a minti na 70, yayin da Idrissa Gueye ya kara ta biyu a minti na 76.

Ana haka ne dai Blati Toure ya farke wa Burkina Faso kwallo daya a minti na 82, sai dai Sadio Mane, lamba goman tawagar ta Senegal da ya bayar da taimakon kwallon da Idrissa Gueye ya jefa, ya kara kwallo ta uku a minti na 87, kuma a haka aka karkaren wasan.

A gobe Alhamis ce za a fafata wasan kusa da karshe na Gasar Cin Kofin Afirka tsakanin kasar Kamaru mai masaukin baki da kasar Masar a wasan da ake wa kallon wasa mafi zafi a gasar a filin wasa na Olembe da ke birnin Yaounde.

Kasar Kamaru mai masaukin baki tana matukar tashe a wannan gasar, inda ba ta rasa wasa ko daya ba tun fara gasar har zuwa wannan mataki na wasan kusa da karshe.