✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sevilla ta dauki Martial a matsayin aro daga Manchester United

Dan wasan zai zauna a Sevilla a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasanni ta bana.

Dan wasan gaban Manchester United, Anthony Martial ya sauya sheka zuwa kungiyar Sevilla da ke kasar Spain a matsayin aro, har zuwa karshen kakar wasanni ta bana.

Kungiyoyin sun kulla yarjejeniyar sauya shekar dan wasan ne bayan shafe tsawon lokaci suna tattaunawa, inda Sevilla ta amince za ta ci gaba da biyan albashin dan wasan.

Tuni dai Martial ya tafi kasar Spain inda za a masa gwajin lafiya, kafin daga bisani ya fara atisaye a ranar Alhamis.

Anthony Martial, wanda dan asalin kasar Faransa ne ya gaza haska tauraronsa a Manchester United tun bayan da kungiyar ta saye shi daga Manaco a 2017.

Hakan ya sanya dan wasan rasa gurbi a tawagar ’yan wasan kasar Faransa a gasar cin kofin duniya da aka yi a kasar Rasha

Dan wasan ya ci gaba da fuskantar kalubalen rashin buga wasa tun daga kan Mourinho, Solskjaer har zuwa kan kocin Manchester United na yanzu, Ralf Rangnick.