✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shafin Trust Plus: Gayyata ta musamman ga masu bibiyarmu

Shafin Trust Plus zai rika ba da wani kaso ga mambobi bisa tsarin biyan kudi.

Kamfanin Media Trust, mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya, ya kaddamar da sabon shafin Trust Plus, wani dandamali na zamani (digital) wanda zai rika ba da wani kaso na musamman ga mambobi bisa tsarin biyan kudi.

Kodayake babu shinge na biyan kudi don samun dama ga abubuwan da suke ciki na musamman, wannan wani yunkuri ne na kokarin hada ’yan jarida da aikin jarida tare da masu sauraro ta hanyar da’irar tuntuba.

Shafin yana ba wa ’yan jarida ko masu amfani da kafofin watsa labarai da kuma jama’a damar ba da gudunmawa ga abin da ’yan jarida suke yi ga ’yan jarida don amfani da kwarewa wajen samar da ingantattun bayanai a kafofin watsa labarai da suka dace da al’umma.

Wannan sabon tsari yana nufin canja tunanin cewa aikin jarida fasaha ce ga mutanen da aka horar kawai da su za su iya shiga.

Ana nufin samar da ingantattun abubuwan watsa labarai ga al’umma, ta al’umma kuma tare da al’umma.

Wannan aikin ya yi daidai da manufofin Kamfanin Media Trust Limited na samar da ingantattun labarai da za su kasance masu fa’ida ga jama’a da kuma dukkan masu ruwa-datsaki.

Farawa da jaridar mako-mako ta Weekly Trust, wadda aka fara bugawa a 1998, kamfanin ya ci gaba da fito da nau’o’in da suka dace da bukatun al’umma.

Jaridar yau da kullum ta Daily Trust ta fara fitowa a shekarar 2000, sai Sunday Trust da Aminiya suka biyo baya a 2006, yayin da sauran samfuran da suka hada da Tambari, Kilimanjaro, Golf, Teen Trust, Trust Sport, Daily Trust Online, Trust TV da kuma yanzu Trust Plus suka fito don hidima ga al’umma daban-daban.

Kamfanin MTL ya ci gaba da habaka yanayin watsa labarai da kuma ci gaba da canzaja daidai da fasahar da take tasowa da kuma bukatun al’ummarmu da makaranta da masu sauraronmu.

A cikin wannan zamani da kafofin sada zumunta suke watsa labaran da ba su da sahihanci, wannan shafi na Trust Plus an yi shi ne don samar da labarai tare da samar da wani amfani wanda zai kasance wani canji ne, na asali daga fitowar labarai ta hanya daya.

An tsara aikin bisa ka’idar cewa idan al’umma ta shiga cikin tsarin labaran, dole ne samfurin ya kasance ya dace kuma yana da fa’ida ga al’ummar.

Hakan zai karfafa aikin jarida wanda ya sha fama da kalubale da wahala daga ikon masu barna da rikice-rikicen rashin bayanai na gaskiya da rashin amana da rikicin kudi ga kuma matsalar cutar Kwarona.

Wannan aikin, ya kasance ne da tallafin Bunkasa Labarai na Gidauniyar MacArthur kuma kofa a bude take ga masu karatu a fannoni daban-daban.

Fitattu – daga cikinsu masu ilimi da kwararru a fannoni daban-daban da manyan jami’an gwamnati da wadanda suke cikin kungiyoyin diflomasiyya – suna iya shiga cikin shafi na Trust Plus Community, kuma su mallaki tsarin samar da labarai ta hanyoyi uku:

Ba da gudunmawa ga ra’ayoyi da labarai ga ’yan jaridarmu don yin bincike da bugawa da rubuta labarai masu ilimantarwa wadanda suke ba da haske game da al’amuran yau da kullum a cikin kasa, ko yin sharhin a kan abubuwan da suke cikin dandamalin don ba wa ’yan jaridarmu damar samar da ingantattun sigogi ga irin wadannan rahotannin.

Ta hanyar wannan shafin labarai na Trust Plus, za a ci gaba da samar da ingantattun rahotanni da bincike mai zurfi tare da samar da bayanai da kuma mai da hankali a kan samar da mafita ga kalubalen da wani yanki yake fuskanta da zamantakewa da kuma kalubalen tattalin arziki.

Wani nau’in wannan yunkurin shi ne an bude wannan shafi na Trust Plus ga daliban Najeriya da ke nan gida da kuma kasashen waje, hakan zai bai wa daliban damar yin rubutu game da rayuwar da suka yi a jami’a da abubuwan da suke tsammani daga gwamnati da al’umma, da kuma abin da suka amfana daga jagorar aiki da ba da shawara.

Wannan shafi zai bai wa dalibai damar canja irin tsarin ko gyare-gyaren da suka dace tun suna jami’a.

Matasa suna da kashi 60 cikin 100 na yawan jama’ar kasar nan. Kuma wannan sashi na kasar nan shi ne yake fama da rashin aikin yi da kuma matsalar rashin zaman lafiya.

Don tabbatar da ganin an samu hanyar da wannan yawan jama’a zai amfana, wannan shafi na Trust Plus zai sa matasa su aiwatar da wani tsari ta yadda ya kamata a samar wa al’umma wani kebabben abu na game da sana’o’i da fasaha da yanayin rayuwa da alaka, a matsayin hanyar samar da ingantaccen jagoran da ake bukata don matasa su rayu, rayuwa mai ma’ana.

Kayayyaki

Aikin wannan shafi ya kunshi manyan samfura hudu wato: Rahoto na musamman da gudanar da bincike/daidaito: Samar da rahotanni na musamman a aikin jarida da yin bincike, musamman a kan abubuwan da suka shafi mata.

Shafin Dandalin Matasa: Bugawa sau biyu a mako wanda yake nufin cim ma muradun matasa ’yan bana-bakwai da kuma masu fasahar zamani.

Shafin Dandalin Samun aiki: Bugawa sau biyu a mako wanda yake nufin mutanen da suke aiki.

Abubuwan da za su hada da ayyuka da kwarewa da samar da horo tare da kasidu don habaka ci gaban aiki.

Mambobi a harabar manyan makarantu: Kungiyoyin dalibai a duk manyan cibiyoyin ilimi a ciki da wajen Najeriya, don su rika ba da rahoto ga jaridar Daily Trust ta wani shiri a kan abubuwan da suke faruwa har a harabar cibiyoyin karatu a Najeriya.

Amfanin shirin

1. Haduwa: Mambobi za su samu damar kasancewa cikin masu rubuce-rubucenmu, masu fallasawa da kuma kwararru.

2. Samun dama: Mambobi za su samu dama ta musamman ga wasu samfuran zamani da aka zaba irin su (e-paper, wasikar mambobi, shirin Podcasts da dandalin matasa da kuma na samun aiki).

3. Shiga ciki: Mambobi za su iya ganawa da editocinmu da masu dauko rahoto kuma su kasance cikin aikin jarida da muke yi

4. Ragi: Mambobi za su samu rangwame a duk lokacin da suka saya daga shagunanmu

5. Damarmarki: Mambobi suna da wata kebantacciyar dama ta musamman ga abubuwan sadarwarmu da damar aiki da damar samun horo da shiga gasa.

Mambobi kuma za su amfana daga horarwarmu ta yau da kullun da musayar ilimi da zama da kwararru, da inganta fasaha da za a yi rika yi lokaci-lokaci.

Ba da gudunmawa ga wannan shafi na labaran zamani Trust Plus ba kawai zai tsaya ga taimakawa wajen samar da kudaden shiga ba ne, don mu ci gaba da kasancewa cikin kasuwanci ba, a’a hakan wata hanya ce ta kasancewa a cikin wannan dandali.

Ta hanyar shiga da ba da gudunmawa ga shafin Trust Plus, mambobi suna nuna cewa sun raba kimar bincike da samar da mafita a aikin jarida, kuma ya zama jagorar aiki ga dalibai da kuma kyakkyawar hanyar shigar da matasa a cikin al’ummar da take lalata da gurbata zamantakewa don kawo gyara.

Haka nan batun hadin gwiwa ne a tsakanin shafin da masu karatunsa.

Kuma wannan ra’ayin ya dace da zamanin biyan kudi ta Intanet a bisa tsarin da ya dace da habaka fasaha.

Ingantatcen aikin jarida yana bukatar kashe kudi sosai, ya kunshi bincike da sosai da tafiyetafiye da daukar kwararru, da sayen kayan aikin jarida na zamani.

Don haka ana bukatar mambobin wannan shafi su ba da gudunmawar mafi karanci ta Naira 1,000 kowane wata don wannan aiki, don ci gaba da gudanar da shafin Trust Plus.

Wannan gudunmawar ba a bukaci dalibai da marasa aikin yi su ba da gudunmawar kudi kafin su zama mambobi ba.

Don shiga cikin tsarin Trust Plus, za ku iya shiga ta wannan adireshi kamar haka: https:// membership.dailytrust.com/ kuma bi ta hanyar aiwatarwa don yin rajista da kuma yin rajista ga al’umma ko kuma bayar da gudunmawarku ta kudi.

Mun gode kan sha’awarku wajen tallafa wa shafin Daily Trust Plus.

Don karin bayani tuntubi: [email protected] WhatsApp: +234 806 990 3410