✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shahararren Dan Dambe, Usaini Mai Gidan Sama, ya rasu

Usaini Maigidan Sama ya rasu bayan an yi masa tiyata a asibiti.

Allah Ya yi wa shararren dan damben gargajiya, Usaini Maigidan Sama, rasuwa a Karamar Hukumar Sumaila ta Jihar Kano sakamakon gajeruwar rashin lafiya.

Wani dan uwan marigayin mai suna Danladi Usman ya shaida wa Aminiya  cewa Usaini Maigidan Sama ya rasun ne a kauyensu mai suna Ziyara a yankin Kula.

Ya ce, “Usaini Maigidan Sama Allah Ya yi masa rasuwa jiya Asabar a garinsu mai suna Ziyara, sanadiyar tiyata ta ciwon kaba da aka yi masa.”

– Rayuwar damben Maigidan Sama

Marigayin kafin rasuwarsa da kama sana’ar dambe ya yi rayuwarsa ce a garin Kula, kafin daga baya ya fara zuwa wasu garuruwa.

“Ya tafi sana’ar yin dambe shekara 30 ke nan, ya kuma fara harkar dambe a Garin Gusau, hedikwatar Jihar Zamfara, ya kuma ketara har Maradi a Jamhuriyar Nijar,” inji Danladi.

A cewarsa, damben da Marigayin Maigidan Sama ya fara yin tashe da shi shi ne, “Lokacin Alhaji Dan Kure, shi ne damben da ya yi ya shahara ya daukaka.

“Ya samu nasarorin masu dimbin yawa lokacin da ya yi ganiyarsa.”

Abokan dambensa sun hada da “Alhaji Kore, na Karkar, Hardon Bandi, Tsoho na Dayyabu, Danladi Dan Mutanen Daura da Mahaukaci na Sarkin Lere.

“Akwai ma Sama’ila Mai Daushe, akwai Cajina, shi ne abokin dambensa na farko, dama kuma shi kadai ya rage a abokan dambensa, shi yana raye.

“Yauwa akwai Duna Mai Carbi, akwai Ada na Janruwa,” inji Danladi.

Sai dai wata majiyarmu ta ce, “Ada na Janruwa ba abokin Damben Usaini Maigidan Sama ba ne, abokin damben yaronsa ne.”

Daga cikin yaran Usaini Maigidan Sama akwai Ado Dan Kwaure da Kutama da Abdu Maibugu da Sani da kuma Dan China.