✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shan sigari na kashe ’yan Najeriya 29,000 a shekara

Abin da gwamnati ke samu daga harajin sigarin bai wuce kashi 10 cikin 100 na kudin da take kashewa ba.

Wani bincike da cibiyar nazarin tattalin arzikin Afirka ta yi ta gano shan taba sigari na kashe ’yan Najeriya dubu 29 duk shekara.

Mataimakin mai bincike a cibiyar na Najeriya, Austin Iraoya, ne ya bayyana hakan inda ya ce Najeriya na kashe akalla Naira biliyan 526 duk shekara kan larurar da ke da alaka da shan sigari.

“Yawanci kudaden sun fito ne daga aljihun gwamnati, hakan ne ya sa ya zamo babbar matsala ga tattalin arzikin kasa.

“Abin dubawa a nan shi ne, abin da gwamnati ke samu daga harajin sigarin bai wuce kashi 10 cikin 100 na kudin da take kashewa ba”, in ji Iraoya.

Wannan bayani na Iraoya yayi shi ne ranar Litinin a Abuja a taron manema labarai na ranar tunatarwa kan Illar zukar Sigari ta Duniya.

Haka zalika shi ma Babban Daraktan Hukumar Tabbatar da Bin Doka da Samar da Hadin Kan Afirka, Akinbode Oluwafemi, ya ce shan sigari a yankin na karuwa, kuma Najeriya ce ke kan gaba, inda take shigo da ita daga kasashe 44 na duniya.

Yadda kamfanonin waje suka koma shigo da sigari Afirka

Ya ce: “Abin damuwa ne yadda tsauraran dokoki suka sanya aka daina shigar da sigarin kasashen Yammacin duniya, inda kamfanonin suka koma kawo su kasashe irin su Najeriya.

Ya ce duk da hukumar kula da kafafen sadarwa ta kasa ta hana watsa shirin nan na BB Naija da yara da manya ke kallo a kasa, masu fitowa a cikinsa na shan sigarin a fili, da kuma tallata shi.

Ita ma Daraktar Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya reshen Afirka, akwai bukatar kasashen Afirka su kara haraji kan shigo da sigarin da kuma kasuwancinsa.

Illolin sigari ga Muhalli

A bangaren muhalli kuwa daraktar ta ce noman sigari na janye ruwa, wanda a yanzu yake wahala a sassan yankin, ga kuma gurbata iska, da ruwan sha.

Haka kuma ta ce manomansa na da hadarin da sinadarin nicotine da sigarin ke dauke da shi, yake haifarwa idan ya taba fata, musamman a lokutan da ganyayen suke tofowa, da ma kurarsa.