✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shari’ar Abduljabbar ta danne ta Dan Sarauniya a Kano

Kotun ta yi la’akari da cewar ana jibge jami’an tsaro a shari’ar Abduljabbar.

Kotun Majistiri mai lamba 58 da ke zamanta a Nomanslan a Jihar Kano ta dage zaman da za ta yi a gobe Alhamis 3 ga watan Fabrairu a kan zargin da ’yan sanda ke yi wa tsohon Kwamishinan Ayyuka, Injiniya Mu’azu Magaji saboda shari’ar Malam Abduljabbar Nasiru Kabara da za ta ci gaba da gudana.

Mai Shari’a Aminu Gabari ne ya dage zaman daga 3 ga wata zuwa 4 ga watan na Fabrairu sakamakon yanayin tsaro kuma a ranar 3 ga watan ne za a ci gaba da shari’ar Abduljabbar Nasiru Kabara.

Kotun ta yi la’akari da cewar ana jibge jami’an tsaro a shari’ar Abduljabbar haka zalika ita ma shari’ar tsohon Kwamishinan Ayyukan da aka fi sani da Dan Sarauniya tana bukatar a tanadar mata jami’an tsaro.

Barista Garzali Datti Ahmad wanda shi ne Lauyan Dan sarauniya, ya bayyana cewa duk da cewar ba su ji dadin wannan al’amari ba amma sun karbi uzurin kotun duba da cewa an danganta lamarin da batun tsaro.

“Babu yadda za mu yi tunda batu ake yi na tsaro sun nuna cewa ba za su iya samar da tsaro a kotunan biyu ba don haka mun karbi uzurinsu. Allah Ya kai mu ranar Juma’ar.”

Ana dai zargin Dan Sarauniya da laifin cin mutunci da kuma bata sunan Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Ganduje ta hanyar yada wani hoto a shafinsa na Facebook da ke nuna cewa yana neman mata.

Ana iya tuna cewa, a ranar Juma’a 16 ga watan Yulin bara ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Sheikh Abduljabbar a gaban kotu bisa zargin batanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.